Najeriya-Biafra

Najeriya ta yi watsi da ayyana gwamnatin Biafra da Dokubo ya yi

Mujaheed Dokubo Asari. jagoran 'yan tsageran Neja delta a Najeria.
Mujaheed Dokubo Asari. jagoran 'yan tsageran Neja delta a Najeria. © panafricanvision.com

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da ikirarin Asari Dokubo na kafa gwamnatin al’ada ta Biafra, inda ta ke cewa ya yi hakan ne domin neman suna.

Talla

Ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed ya ce gwamnatinsu ba za ta bari wasu su dauke mata hankali da batutuwan da basu da tasiri ba.

Mohammed ya ce idan Dokubo na bukatar kafa irin wannan gwamnatin mara tasiri, matakin ba zai dauke hankalin gwamnatin su kan ayyukan da suke gudanarwa ba, saboda suna da gagarumin aikin da suka mayar da hankali akai.

Ministan ya ce basu da lokacin da zasu bata wajen karkata zuwa wurin mutanen da ke bukatar suna irin su Asari Dokubo, saboda haka suna daukar ikrarin.

Asari Dokubo dake jagorancin kungiyar dake fafutukar ‘yantar da Naija Delta ya bayyana nada kan sa a matsayin jagoran gwamnatin al’ada ta Biafra tare da sanar da sunayen wasu mutane a matsayin mukarraban sa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.