Najeriya - Tattalin Arziki

Tsadar rayuwa da rashin aikin yi sun yi kamari a Najeriya - Rahoto

Wasu 'yan Najeriya yayin zirga-zirgar yau da kullum a birnin Legas.
Wasu 'yan Najeriya yayin zirga-zirgar yau da kullum a birnin Legas. © Akintunde Akinleye/Reuters

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karin marasa aikin yi, adadin da ya karu da sama da kaso 33 cikin 100.

Talla

Wannan shi ne kaso mafi munin da aka taba gani na marasa aikin yi kasar cikin shekaru 13.

Cikin rahoton da ta fitar, hukumar kididdigar Najeriya ta kara da cewar baya ga matsalar ta rashin aikin yi, a farkon shekarar bara, hauhawar farashi da tsadar rayuwa a kasar ya karu da kaso 16.47 a watan Janairu, yayin da ya karu zuwa kaso 17.33 a watan Fabrairu.

Daga Abuja, wakilinmu Muhammad Kabiru Yusuf ya aiko mana da rahoto.

Rahoto kan karuwar matsalolin rashin aikin yi da tsadar rayuwa a Najeriya
Rahoto kan karuwar matsalolin rashin aikin yi da tsadar rayuwa a Najeriya

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.