Najeriya-Lagos

Jihar Lagos ke dauke da kashi 30 na masu shaye-shaye a Najeriya- Marwa

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo Olu tare da shugaban hukumar NDLEA Janar Buba Marwa.
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo Olu tare da shugaban hukumar NDLEA Janar Buba Marwa. © RFI Hausa/Lagos state government

Shugaban hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya Janar Muhammadu Buba Marwa ya ce akalla mazauna Lagos miliyan 4 da rabi ke mu’amala da miyagun kwayoyi a birnin, abinda ke nuna karuwar matsalar da ta addabi Najeriya baki daya.

Talla

Yayin da ya ke ziyarar gani da ido tun bayan nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya masa, Janar Marwa ya bayyana birnin Lagos a matsayin Jihar da ake samun kashi 30 na masu amfani da miyagun kwayoyin.

Shugaban Hukumar ya ce daga cikin mutane miliyan 15 da aka yi kiyasin suna mu‘amala da miyagun kwayoyin wajen sha da fataucin su, miliyan 4 da rabi na zama ne a Lagos, yayin da sauran kuma suka watsu zuwa sassan Najeriya.

Janar Marwa ya baiwa jami’an umurnin kara kaimi wajen shawo kan matsalar musamman ganin an kama da hukunta masu safarar kwayar da kuma masu sayar da ita.

Shugaban Hukumar ya danganta matsalar ta Lagos da yawan gidajen sayar da magunguna wadanda basu da rajista da Hukuma da yawan su ya kai kusan miliyan guda.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.