Najeriya-Tattalin arziki

Najeriya na bukatar samar da guraben ayyuka miliyan 5 duk shekara- WTO

Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Ngozi Okonjo-Iweala
Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, Ngozi Okonjo-Iweala Fabrice COFFRINI AFP/Archivos

Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya Ngozi Okonjo-Iweala ta ce Najeriya na bukatar samar da ayyukan yi akalla miliyan 5 kowacce shekara na shekaru 10 a jere domin shawo kan matsalar rashin ayyukan yin da suka addabi jama’ar kasar.

Talla

Tsohuwar ministar Najeriyar ta ce ya zama wajibi gwamnatin kasar ta samar da yanayi mai kyau da zai haifar da ayyukan yi musamman ga matasa, yayin da ta yi tsokaci kan bunkasa bangaren masana’antu inda ta bukaci masu jagorancin yankin da su tashi tsaye.

Ngozi-Iweala tace tun daga shekarar 2016 tattalin arzikin Najeriya ya fara samun matsala sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Shugabar Hukumar WTO ta ce yanzu haka tattalin arzikin kasar na fuskantar matsaloli saboda rashin yin sauye sauyen da ake bukata abinda ya sa duk lokacin da farashin mai ya fadi sai kasar ta girgiza.

Ngozi-Iweala ta bai wa Najeriya shawarar sake fasalin tattalin arzikin ta da kuma tsarin da zai taimaka mata samun cigaba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.