Yan bindiga sun bude wuta kan tawagar Sarkin Birnin Gwari dake Najeriya

Wasu yan bindiga dauke da makamai a Najeriya
Wasu yan bindiga dauke da makamai a Najeriya REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Rahotanni daga Jihar Kadunan Najeriya sun ce 'Yan bindiga a yammacin jiya sun bude wuta kan tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari na biyu amma bai samu rauni ba.

Talla

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar lokacin da Yan bindigar suka bude wuta kan tawagar motocin Basaraken dake kan hanyar zuwa Kaduna, Sarkin baya cikin motar.

Direban Sarkin Umar Jibril ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yake cewa lokacin da Yan bindigar suka tare hanya da itatuwa suka kuma bude musu wuta, Sarkin baya cikin motar sa.

Direban yace lokacin da aka bude musu wutar basu tsaya ba, kuma kokarin harbin sa ya ci tura inda harsashi ya wuce kusa da kan sa.Jibril yace banda yan raunuka da wasu dake cikin tawagar suka samu da kuma fasa musu gilasan motocin su, babu wanda ya samu wani babban rauni.

Karamar hukumar Birnin Gwari dake Jihar Kaduna na sahun gaba wajen fuskantar hare haren Yan bindiga, inda ko a ranar litinin sanda aka kai hari wata makarantar Firamare inda aka sace malamai da daliban su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.