Najeriya - Kano

Kano: Mutane 4 sun mutu daruruwa sun jikkata bayan shan gurbataccen lemu

Wasu masu sana'o'i a jihar Kano dake arewacin Najeriya.
Wasu masu sana'o'i a jihar Kano dake arewacin Najeriya. © Luc Gnago/Reuters

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 4 da kuma jikkatar wasu kusan 300 sakamakon shan wasu nau’ikan lemu da ake zargin gurbatattu ne.

Talla

A karshen makon jiya ne dai aka samu barkewar wata cuta mai haddasa aman jini da fitsarin jini a sassan jihar ta Kano bayan amfani da ruwan wata rijiya da kuma shan wasu sinadaran hada ababen sha da wasu mutane suka yi

Domin sauraron rahoton da wakilinmu Abubakar Isah Dandago ya aiko mana daga Kanon sai a latsa alamar sautin dake sama.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.