Najeriya-Buhari

Buhari ya koka da yadda makamai ke ci gaba da kwarara Najeriya daga Libya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa kan yadda aka ci tgaba da fuskantar matsalar safarar miyagun makamai zuwa cikin kasar daga Libya duk da rufe iyakokin da Najeriyar ta yi na dogon lokaci a wani yunkuri na dakile matsalar da ke barazana ga tsaron kasar.

Talla

Yayin da ya ke karbar Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a yankin Afirka ta yamma, Mohammed ibn Chambas wanda ya kawo karshen aikin sa a yankin, shugaba Buhari ya sake jaddada matsayin sa cewar rashin zaman lafiyar Libya zai cigaba da yin illa ga kasashen da ke yankin Sahel.

Buhari ya ce duk da rufe iyakokin da Najeriya ta yi na shekara guda babu abinda ya sauya, ganin yadda aka yi ta shigar da makamai zuwa cikin kasar.

Chambas wanda ya yabawa Najeriya da Buhari kan taimakon da suka bashi wajen gudanar da aikin sa, ya ce Najeriya na taka gagarumar rawa wajen yaki da ta’addanci a Yankin Tafkin Chadi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.