Najeriya-ICG

Shirin sauya tunanin tubabbun mayakan Boko Haram baya aiki a Najeriya- ICG

Wasu daga cikin tubabbun ‘yan kungiyar boko haram.
Wasu daga cikin tubabbun ‘yan kungiyar boko haram. Daily Post

Kungiyar International Crisis Group da ke sanya ido kan rikice-rikice ta ce shirin Gwamnatin Najeriya na bai wa mayakan boko haram damar aje makaman su domin samun afuwa da kuma horo na fuskantar matsaloli duk da nasarorin da aka samu.

Talla

Sanarwar da kungiyar ICG ta gabatar ya zargi sojojin da ke kula da shirin afuwar a Najeriya da kama mutanen da babu ruwan su da rikicin boko haram suna sanya su cikin shirin, abinda ya ke kara yawan su da kuma haifar da janyewar masu bada gudumawar kudade wajen tafiyar da shi.

Kungiyar ta kuma ce sojoji na azabtar da mutanen da ake zargi bayan sun fada hannun gwamnati, abinda ke haifar da tsoro ga wadanda suke shirin aje makaman su.

Sanarwar kungiyar ta ce wadanda suka ci gajiyar shirin na kuma fuskantar kalubalen adawa daga manyan 'yan siyasa da sauran jama’a dangane da ko ya dace wadanda suka aje makaman su su ci gajiyar afuwar gwamnati da kuma taimakon masu bada agaji, musamman a dai dai lokacin da mayakan ke kara kaimi wajen kai hare haren su.

ICG ta bayyana cewa wannan ya sa shirin ya gaza wajen cimma muradun sa.

Domin sake fasalin shirin wajen janyo hankalin mayakan su aje makaman su domin mika kai da kuma samun taimakon kasashen duniya, kungiyar ta ce dole sai hukumomin Najeriya sun nuna yadda shirin zai horar da tubabbun mayakan da kuma yadda za su shiga cikin jama’a ba tare da fuskantar matsala ba.

Kungiyar ta ce shirin zai samu karbuwa ne idan gwamnati ta inganta yadda ta ke tantance fararen hula da tsoffin mayakan da kuma inganta inda ake horar da su domin mayar da su cikin al’umma.

ICG ta ce shirin na da damar taka rawa wajen kara yawan mayakan boko haram da ke rungumar sa, amma muddin ba’a sake fasalin sa ba, shirin zai rasa taimakon kasashen duniya da kuma karbuwar sa a cikin gida.

Mun yi iya bakin kokarin mu domin jin ta bakin Kakakin ma’aikatar tsaron Najeriya da ke kula da shirin Janar Nwachukwu amma hakarmu bata cimma ruwa ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.