Najeriya

Ganduje ya sha alwashin hukunta masu hannu wajen zargin sa da karbar daloli

Gwamnan jihar Kano  Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Premium Times

Gwamnan Jihar Kano dake Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu yana da hannu wajen fitar da faifan bidiyon dake nuna shi yana sanya daloli a cikin aljihun babban rigar sa.

Talla

Ganduje ya bayyana faifan bidiyo a matsayin yarfe da ake neman bata masa suna, kuma tuni aka kaddamar da bincike akai domin gano wadanda suke da hannu a ciki.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Gwamnan yayi alkawarin cewar bidiyon karya ne tsagoranta domin babu wani abu haka da ya faru, yayin da yake bayyana shi a matsayin yunkurin hana shi takarar neman wa’adi na biyu wanda tuni ya samu nasara akai.

Jaridar Daily Nigerian ce ta wallafa hotan bidiyon wanda ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Najeriya, yayin da Editan Jaridar Malam Jaafar Jaafar ya kuma je Majalisar dokokin Kano domin kare shaidun da suke da shi dake tabbatar musu da labarin.

Tuni gwamnatin Jihar Kano taje kotu dangane da lamarin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.