Najeriya-'Yan bindiga

Gwamnan Jihar Benue ya tsallaka rijiya da baya

Tuni dai aka Jibge tarin Jami'an tsaro a Jihar ta Benue don tabbatar da tsaro
Tuni dai aka Jibge tarin Jami'an tsaro a Jihar ta Benue don tabbatar da tsaro AFP

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu 'Yan bindiga sun kai hari kan tawagar motocin Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom a kan hanyar Tyomu dake karamar hukumar Makurdi amma babu abinda ya same shi. 

Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar tace Gwamnan na komawa Makurdi daga Gboko ne lokacin da Yan bindigar suka budewa tawagar motocin sa wuta.

Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom.
Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom. Leadership Newspaper

Shaidun gani da ido sun ce an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron dake rakiyar Gwamnan da Yan bindigar lokacin da aka kai masa harin.

Jihar Benue na daya daga cikin Jihohin Najeriya dake fama da matsalar tsaro, inda ko a kwanakin da suka gabata sanda aka hallaka dan uwan tsohon Gwamnan Jihar.

Gwamnan Ortom ya dade ya na gabatar da korafi kan matsalar tsaron da Jihar sa ke fuskanta inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta baiwa jama’ar jihar damar mallakar bindiga domin kare kan su.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.