Najeriya

Idan Najeriya ta rushe, daukacin bakaken fatar duniya sun gaza - Alake

Sarkin Yarbawa Adeyeye Enitan Babatunde Ogunwusi, a Najeriya
Sarkin Yarbawa Adeyeye Enitan Babatunde Ogunwusi, a Najeriya © Page Facebook @olojofestival

Babban Basaraken Jihar Ogun da ake kira ‘Alake of Egbaland’ Oba Adedotun Aremu Gbadebo  yayi kira ga masu fafutukar ganin an raba Najeriya da suyi watsi da bukatar su, inda yake cewa idan Najeriya ta rushe a matsayin kasa guda daukacin bakaken fatar dake doron kasa sun gaza.

Talla

Basaraken yace wadanda ke kada gangar yaki a Najeriya ba wai suna kokarin haifar da rudani ne a kasar ba, harma da nahiyar Afirka baki daya.

Kayan al'adun gargajiya na Yarbawa
Kayan al'adun gargajiya na Yarbawa Olivier Desart/Musée du Carnaval et du Masque, Binche

Oba Gbadebo yace ya zama dole ‘yan Najeriya daga kowacce kabila ko bangaren addini ko siyasa suyi aiki tare saboda hadin kan kasa da kuma cigaban ta, yayin da yake cewa tafiyar kasar a matsayin dunkulalliya ya fi alheri maimakon rarraba ta.

Basaraken yace Najeriya ba zata iya jurewa wani sabon yakin basasa ba, yayin da babu wata kasa a duniya ayau da zata iya karbar baki sama da miliyan 250 da zasu bar Najeriya a matsayin yan gudun hijira.

Oba Gbadebo ya basa shawara ga al’ummar kasar da su dinga kallon kan su duk inda suka shiga a matsayin Yan Najeriya masu jini guda.

Sarkin yace babu wata kasa a duniya da zata iya ciyar da Yan Najeriya miliyan 250 idan an samu tashin hankali, domin kuwa a cikin kwana biyu za’a cinye abincin kasar.

Basaraken yace ya zama dole bangarorin kasar suyi aiki tare domin shawo kan dimbin matsalolin da suka addabe ta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.