Najeriya-Sokoto-APC

APC na kan hanyar rugujewa- Gwamna Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Aminu Tambuwal
Gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Aminu Tambuwal RFI Hausa

Gwamnan Jihar Sokoto da ke Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya ce nan ba da dadewa ba Jam’iyyar APC za ta rushe saboda rikice-rikicen da suka dabaibaye ta.

Talla

Yayin da ya ke kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomi a jiharsa wanda Jam’iyyar APC ta janye saboda abin da ta kira shirin magudin da Jam’iyyar PDP ta yi, Tambuwal ya ce APC ta janye daga zaben ne saboda rikicin cikin gidan da ya mamaye ta a matakin kasa da jihohi.

Tambuwal ya ce babu abin da gwamnatin APC zata nuna a matsayin nasarar da ta samu tun daga shekarar 2015 da ta karbi mulki.

Gwamnan ya ce wadannan matsalolin cikin gida da suka mamaye Jam’iyyar za su kai ga rushewar ta nan bada dadewa ba.

Tambuwal wanda ya lashe zaben shekarar 2015 a karkashin Jam’iyyar APC daga bisani ya sauya sheka zuwa PDP.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.