Najeriya

Najeriya ta samu koma-baya a jerin kasashen da al'ummarsu ke farin ciki

Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya.
Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya. Reuters / Akintunde Akinleye

Majalisar dinkin duniya ta sanya tarayyar Najeriya a mataki na 116 cikin jerin kasashen da al’ummar su suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa.

Talla

Ta cikin rahoton da majalisar ta fitar, ta bayyana cewa a binciken da ta gudanar a bana, Najeriya ta sami koma baya, kan matakin da take a bara.

A rahoton banan da hukumar ta fitar, ta sanya kasar Finland a matsayin kasar da al’ummar ta suka fi na kowacce kasa farinciki da jin dadin rayuwa, yayin da Denmak ke biye mata baya, sai kuma Iceland da Netherland a mataki na uku da hudu.

Kasashen da al’ummar su suka fi kasancewa cikin tasku da tsananin rayuwa, sun hadar da Afghanistan da Lesotho da Botswana da Rwanda da kuma Zimbabwe.

New Zealand ce Kasar da ta fi kowacce kula da walwalar al’ummar ta a Nahiyar turai a yayin da Mauritius ta fi kowacce kasa sanya ‘yan kasar ta cikin farinciki da kula da jin dadin su a Nahiyar Africa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.