Yan Najeriya na fuskantar hau-hawan farashin kayakin masarufi
Wallafawa ranar:
A Najeriya, yanzu kam ana fuskantar hau-hawan farashi kayakin masarufi da ba a taba ganin irin sa shekaru 15 da suka gabata.
Rahoto da jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar ta ruwaito na dada nuni cewa ta bangaren farashin abinci an samu kari na kusan kashi 27 cikin dari a watan fabrairu shekarar bana.
Hukumar auna cigaban tattalin arziki ta kasar ta bayyana irin tashin gauran zabin da farashin kayyakin masarufi suka yi a kasar yanzu haka,inda ta kuma bayyana cewa masu dan karamin hali na cikin wani mauyacin hali.Daya daga cikin sashen da ya fi jin jiki a wannan yanayi shine bangaren kiwon kaji a cewar wannan hukuma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu