Najeriya

Dangi da 'yan Uwan 'yan makaranta da aka sace a Kaduna sun yi zanga-zanga

Harabar wajen makarantar horas da ayyukan gona da raya gandun daji dake yankin Mando a jihar Kaduna a Najeriya.
Harabar wajen makarantar horas da ayyukan gona da raya gandun daji dake yankin Mando a jihar Kaduna a Najeriya. © REUTERS - STRINGER

Iyayen dalibai 39 na makarantar gandun daji ta Najeriya da ke jihar Kaduna da Yan bindiga su ka yi garkuwa da kwanaki goma Sha biyu da suka gabata sun gudanar da zanga zanga domin tirsasawa gwamnati karbo ma su 'yan na su.Aminu Sani Sado daga Kaduna na dauke da rahoto akai.