Najeriya

2023 - Baraka tsakanin Buhari da Tinubu na dada fitowa fili

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu Nigeria Presidency/Handout via Reuters

Yayin da shirin zaben shugaban kasar Najeriya na shekarar 2023 ke kara karatowa, rahotanni daga kasar na nuna cewar ana cigaba da samun baraka tsakanin jiga jigan Jam’iyyar APC mai mulkin kasar, wato shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu.

Talla

Rahotanni sun ce rashin ganin jiga-jigan 'Yan siyasar biyu na ganawa a tsakanin su koda yaushe kamar yadda suka sabayi a shekarun baya sun dada tabbatar da wannan barakar da ake zargi wadda wasu ke danganta ta da yunkurin wasu ‚ya'an Jam’iyyar APC na hana Tinubu takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu © REUTERS/Afolabi Sotunde

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya tace rabon Bola Ahmed Tinubu da fadar shugaban kasa inda yake ganawa da shugaba Muhammadu Buhari akai akai domin tattauna batutuwan da suka shafi kasa da kuma Jam’iyyar ta su tun ranar 7 ga watan Janarun shekarar 2020.

Wannan ya sa masu sharhi ke hasashen samun rashin fahimtar juna tsakanin shugabannin biyu musamman ganin rawar da Tinubu ya taka wajen ganin Buhari ya zama shugaban kasa bayan yayi takara sau 3 ba tare da samun nasara ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani daga cikin iyalan shugaban kasar na cewar shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba wajen wasu mutane kan cewar kada ya goyawa Tinubu baya wajen zama shugaban kasa a shekarar 2023 domin ba zai kare muradun sa ba idan ya samu mulkin.

Jaridar ta kuma ce daya daga cikin 'Yan majalisun zartarwa gwamnatin Buhari ya bayyana cewar shugaban baya ra’ayin takarar Tinubu saboda bai gamsu cewar shi ne yafi dacewa ya gaje shi ba.

Mai magana da yawun tsohon Gwamnan Lagos Tunde Rahman ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar babu abinda ya sauya tsakanin dangantakar dake tsakanin Tinubu da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rahman yace zargin rashin fahimtar junar da ake yi gulma ce kawai domin haifar da rudani, domin kuwa Tinubu mutum ne mai ladabi wanda ya sadaukar da ran sa domin taimakawa Buhari wajen ganin ya aiwatar da manufofin gwamnatin sa da zasu amfani daukacin yan Najeriya.

Kakakin tsohon gwamnan yace amincewa da Buhari yayi dokin shugabancin taron laccar da za’ayi wajen bikin haihuwar Bola Tinubu ta 12 a ranar litinin mai zuwa wata manuniya ce dake tabbatar da dangantakar dake tsakanin su.

Ya zuwa yanzu dai Tinubu bai fito fili ya bayyana aniyar sa ta takara ba, amma tuni kungiyoyi daban daban suka fara tallata shi, domin ganin ya karbu a wurin jama’ar kasa.

Sai dai wasu masu sharhi na cewar yunkurin Hukumar EFCC na gudanar da bincike kan tsohon Gwamnan na Lagos wani yunkuri ne daga Buhari domin hana Tinubu takara a zabe mai zuwa.

Yayin da wasu ke kallon wannan yunkuri na hana Tinubu takara a matsayin cin amana ganin irin gudumawar da ya bayar wajen samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wasu na cewa siyasa ce kawai akeyi, domin lokacin fidda dan takara bai yi ba.

Rahotanni na nuna cewar wasu daga cikin 'Yan arewacin kasar musamman daga bangaren Gwamnonin APC na bukatar ganin yankin ya gabatar da dan takara, yayin da wasu ke bukatar ganin an ramawa kura aniyar ta wajen mayar da mulki kudancin kasar da kuma goyawa Tinubun baya.

Sakataren Jam’iyyar APC a Jihar Lagos Seye Oladepo yace babu wanda zai hana tsohon Gwamnan Lagos takara, yayin da yayi watsi da zargin cewar akwai baraka tsakanin Buhari da Tinubun.

Sai dai wasu masu sa ido na cewa, yayin da Jam’iyyar APC ke hasashen kwashe shekaru 32 a karagar mulki, kin baiwa Tinubu takara a shekarar 2023 na iya kawo karshen ta wajen kafa gwamnatin tarayya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.