Najeriya

Jam’iyyar APC na bukatar shekaru 32 a karagar mulki

'Yan takarar Jam'iyyar APC mai adawa a zaben fitar da gwani a garin Lagos
'Yan takarar Jam'iyyar APC mai adawa a zaben fitar da gwani a garin Lagos Reuters

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na riko Mai Mala Buni ya bayyana cewar jam’iyyar na bukatar zama a kan karagar mulki na shekaru 32 domin fitar da kitse a wuta ta yadda Yan Najeriya zasu ci ribar dimokiradiyya.

Talla

Yayin da yake kaddamar da kwamitin tintiba na Jam’iyyar Buni yace zasu inganta rayuwar Yan Najeriya muddin aka basu wannan damar na jagorancin kasar domin yin wa’adi 8.

Shugaba Buhari da tsohon Shugaban jam'iyyar APC Oshiomhole
Shugaba Buhari da tsohon Shugaban jam'iyyar APC Oshiomhole RFI Hausa

Shugaban Jam’iyyar yace fatar su itace samar da hanyar da zai basu damar yin wa’adi na 6 da 7 da kuma 8 akan karagar mulki domin aiwatar da manufofin su wadanda zasu inganta rayuwar Yan Najeriya.

Buni wanda shine Gwamnan Jihar Yobe yace suna cigaba da samun nasara wajen janyo jiga jigan yan siyasa suna shiga jam’iyyar ta su, yayin da aka kuma baiwa ‘yayan jam’iyyar damar sabunta rajistar su domin cigaba da taka rawa a cikin ta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.