EU ta sha alwashin taimakawa jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina

Gwamnonin jihohin Sokoto Zamfara da Katsina yayin ganawarsu da jakadan kungiyar EU Ketil Karlsen.
Gwamnonin jihohin Sokoto Zamfara da Katsina yayin ganawarsu da jakadan kungiyar EU Ketil Karlsen. © Mohammed Bello

Kungiyar Tarayyar Turai ta sha alwashin ci gaba da taimakawa Jihohin da ke Arewa maso yammacin Najeriya wajen ganin sun shawo kan matsalolin tsaron da suka addabe su tare da kuma kula da mutanen da suka jikkata sakamakon tashin hankalin da ake samu.

Talla

Jakadan kungiyar Turai a Najeriya Ketil Karlsen wanda ya gana da Gwamnonin Jihohin Sokoto da Zamfara da kuma katsina ya ce sun gana ne kan matsalolin tsaron da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya da tashin hankalin da ake samu a yankin Sahel da kuma yaduwar makamai.

Karlsen ya ce suna farin cikin bada gudumawa wajen kawo karshen matsalar garkuwa da mutane da tashin hankali da kuma sake gina yankunan da wadannan matsaloli suka daidaita wajen ganin an sake gina garuruwan da kuma inganta harkar bada ilimi da lafiya tare da kayan more rayuwa.

Jakadan ya ce tuni kungiyar ke taimakawa jama’ar da ke zama a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya da rikicin book haram ya daidaita, yayin da suke kuma kokarin fadada haka.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yace sun nemi taimakon kungiyar kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya tare da kasashen Amurka da Canada da Birtaniya domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabe yankin su.

Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Matawalle da Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da kuma takwaran sa na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.