Najeriya

Kotu ta aike da malamin Jami'a gidan Yari saboda magudin zabe

Jami'an hukumar zabe yayin da suke aikin shirya kayan gudanar da zaben 'yan Majalisu.
Jami'an hukumar zabe yayin da suke aikin shirya kayan gudanar da zaben 'yan Majalisu. REUTERS/Tife Owolabi

Wata Kotu a Najeriya ta daure wani malamin Jami’ar Calabar Farfesa Peter Ogban shekaru 3 a gidan yari saboda samun sa da laifin sauya alkaluman zaben dan Majalisar Dattawa a Jihar Akwa Ibom.

Talla

Kotun da ke zama a Ikot Ekpene ta samu shehun malamin ne da sauya sakamakon zaben kananan hukumomi guda biyu da suka hada da Oruk Anam da Etim Ekpo domin taimakawa ‘dan takarar Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Godswill Akpabio a zaben shekarar 2019.

Sahihan alkaluman da aka tattara sun nuna cewar Chris Ekpenyong, dan takarar Jam’iyyar PDP ya samu nasarar lashe kujerar, abinda ya sa aka gurfanar da Farfesa Ogban a gaban kotu.

Masu sanya ido kan harkokin zabe a Najeriya sun dadesuna cewa rashin hukunta malaman zabe na daga cikin matsalolin da suka addabi zaben Najeriya wanda wasu ‘yan siyasa ke kallon sa a matsayin a mutu ko ayi rai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.