Najeriya-NDLEA

NDLEA ta sanar da daure mutane 126 cikin watanni 2 saboda safarar tabar wiwi

Jami'an hukumar yaki da sha ko fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a Nigeria
Jami'an hukumar yaki da sha ko fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a Nigeria NDLEA

Hukumar yaki da sha da kuma safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta sanar da daure mutane 126 da aka samu da laifin ta'ammali da miyagun kwayoyi a cikin kasar cikin watanni 2 kacal na wannan shekarar. 

Talla

Hukumar ta ce daga cikin wadannan mutane akwai Musa Ibrahim da aka kama da kilo 40 na tabar wiwi a Jihar Ondo wanda ya samu hukuncin daurin shekaru 16 da watanni 8 a gidan yari, sai kuma Ibrahim Haladu da aka daure shekaru 15 saboda samun sa da sama da kilo 6 da rabi na wiwi a Jihar Bauchi.

Mai Magana da yawun Hukumar NDLEA Femi Babafemi ya ce an kuma daure Haruna Aliyu shekaru 5 a Bauchi saboda samun sa da kilo 609 na tabar wiwi, sai kuma Eke Chibuike da aka daure shekaru 5 a Jihar Plateau saboda samun sa da tramadol da diazepam, sai kuma Idan Kenneth da aka samu da gram 220 na wiwi da gram 4.3 na tramadol da gram 3.3 na rophynol kuma aka daure shi shekaru 2 kan kowacce tuhuma.

Babafemi ya ce daga cikin mutane 126 da aka daure, 18 sun fito ne daga Jihar Kano, 5-5 a Jihohin Imo da Abia, sai kuma 4 a Bauchi.

Shugaban Hukumar Janar Mohammed Buba Marwa ya yabawa jami’an Hukumar da ke jajircewa wajen aikin dakile mu’amala da miyagun kwayoyin da kuma bangaren shari’a da ke tabbatar da hukunta masu aikata laifin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.