Najeriya

'Yan Majalisun kudancin Najeriya sun goyi bayan cigaba da dunkulewar kasar

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin kaddamar da sabon shirin dakile rashin tsaron kafar intanet
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin kaddamar da sabon shirin dakile rashin tsaron kafar intanet © Presidency of Nigeria

'Yan Majalisun Najeriya da suka fito daga yankin kudancin kasar sun bayyana matsayin na cigaba da dorewar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa guda sabanin fafutukar da wasu jama’a keyi na ganin an raba ta domin kafa kasar Oduduwa.

Talla

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan kasar Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana haka yayin gabatar da shugabannin da zasu jagoranci Yan Majalisun da suka fito daga kudancin Najeriya.

Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya. Lagos na daya daga cikin biranen da ake samun masu bahaya a fili
Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya. Lagos na daya daga cikin biranen da ake samun masu bahaya a fili Reuters / Akintunde Akinleye

Wannan matsayi na su na zuwa ne sakamakon yunkurin da wani matashi Sunday Igboho keyi na ganin yankin Yarabawa ya balle daga Najeriya wajen cin gashin kan sa, matakin da ya fara samun karbuwa daga wasu yan kabilar Yarabawa.

Tuni matashin Igboho ke zaga jihohin dake kudu maso yammacin Najeriya domin tallata bukatar ta sa, wadda ta kai ga samu tashin hankali a wasu sassan yankin, abinda ya sa wasu Sarakunan Yankin cikin su harda Oni na Ife da Alake na Egbaland suka fara jan kunne akai.

Ko a wannan mako sanda Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya gargadi Igboho da ya kaucewa zuwa jihar sa domin su suna bukatar cigaba da zama cikin Najeriya.

Wannan yunkuri ya fara jefa shakku kan wasu yan Najeriya a daidai lokacin da ake tunanin mayar da mulkin kasar zuwa kudancin kasar a shekarar 2023.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.