Najeriya-Boko Haram

An yi shagulgulan dawowar wutar lantarki a Maiduguri

Titin kashim Ibrahim kenan a birnin Maiduguri.
Titin kashim Ibrahim kenan a birnin Maiduguri. AFP PHOTO / STRINGER

Daruruwan matasa ne su ka fantsama kan tituna su na murnar dawowar wutar lantarki a Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno,  bayan kwashe watanni 2 ba tare da wutar ba, a daidai lokacin da 'yan kasuwa da masu kananan masana'antu ke lissafta asarar da suka yi sanadiyyar rashin wutar. 

Talla

Mayakan Boko Haram ne dai suka kai hari tare da lalata wata cibiyar rarraba wutar lantarki da ke bada wuta ga al’ummomin jihohin Borno da ma wasu sassan jihar Yobe.

Rashin wutar lantarkin ya kassara harkokin rayuwa da tattalin arzikin  jihar da na al’umma. 

Wasu ‘yan kasuwa da mazauna birnin Maiduguri sun shaida wa RFI Hausa irin wahalar da suka sha sakamakon kwashe watanni biyu babu wuta, inda suka ce sun rika dogaro ne da man fetur wajen gudanar da harkokinsu.

Kwararru sun bukaci jami'an tsaro da gwamnati su dauki matakin magance aukuwar matsalar a nan gaba. 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.