Najeriya

Ana cigaba da yiwa jama'a allurar yakar cutar Covid 19 a Najeriya

Allurar Astrazeneca
Allurar Astrazeneca © REUTERS

A Najeriya kusan makonni uku da soma yiwa jama’a allurar rigakafin cutar Covid 19,alkaluma daga hukumar yaki da cuttuka ta kasar na nuni cewa mutane  374.585 ne suka amfana da wannan allura.

Talla

Jihar Kogi kadai ce yanzu haka ba a isa da wannan allura ba ,Faisal Shuaib dake shugabantar  wannan hukuma  ya bayyana cewa ana cikin gyaran dakin ajiye maguguna na jihar ta Kogi,dakin da masu zanga- zanga End Sars suka lallata a baya.

Isowar alluran Astrazeneca a Najeriya
Isowar alluran Astrazeneca a Najeriya REUTERS - ABRAHAM ACHIRGA

Cutar ta Covid 19 ta hallaka akala mutane 2000 a Najeriya, Jihar Lagas da aka fi yawan mutanen da suka kamu da wannan cuta,kusan mutane  92.000  suka amfana da wannan allura,jihar Ogun mutane 36.953, Bauchi 31.321, Kaduna 29.426, Jigawa 22.420 sai Kwara mutane 20.060.Jihohin dake da karancin mutane da suka amfana da wannan allura sun hada da Kebbi mutun daya,Taraba mutun guda sai Abia mutun daya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.