Atiku ya jaddada matsayinsa a kan sayar da NNPC
Wallafawa ranar:
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya sake yin kir da a sayar da kamfanin man fetur na NNPC da matatun man kasar.
A ranar Lahadi ne Atiku ya jaddada wannan kira a matsayin daya daga cikin shawarwarinsa a game da yadda za a shawo kan matsalar rashin aikin yi a kasar.
Kalaman na sa na zuwa ne a matsayin martani ga wani rahoton da kafar yada labaran tattalin arziki na Bloomberg Business ya ruwaito a ranar Asabar da ke cewa nan ba da jimawa ba Najeriya za ta kasance kasar da ta fi kwacce yawan masu zaman kashe wando a duniya da sama da kashi 33 cikin 100.
Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce rashin aikin yi a kasar ya tashi da kashi 33.3 cikin 100 a rubu’in karshe na shekarar da ta gabata, abin da ke nuni da cewa mutane miliyan 23 da dubu dari 2, ko kuma mutum 1 cikin 3 na wadanda suka kai munzulin gabatar da aiki a kasa ba shi da aikin yi ko wata sana’a.
Wannan adadi shine mafi muni a cikin shekaru 13, kuma na 2 a duniya.
A cikin sanarwa da ya fitara ranar Lahadi, Atiku ya ce rahoton na Bloomberg ya nuna cewa bai yi kuskure ba a kan tsokacin da yake yi a game da tattalin arzikin Najeriya.
Atiku ya ce ya sha yin kashedi a game da haka amma aka yi ta jifarsa da munanan kalamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu