Najeriya

Ba zan goyi bayan Buhari ya nemi wa'adi na 3 ba-Ahmed Lawan

Shugaban Najeriya  Mohammadu Buhari
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan yace koda sunan wasa ba zai goyi bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar domin baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari damar neman wa’adin na 3 ko kuma cigaba da zaman sa a karagar mulki bayan shekarar 2023 ba.

Talla

Wata sanarwar da mai magana da yawun sa Ola Awoniyi ya rabawa manema labarai tayi watsi da zargin da ake cewa shugaban Majalisar Dattawan na goyan bayan shirin tsawaita mulkin Buharin.

Mohammadu buhari ,Shugaban Najeriya
Mohammadu buhari ,Shugaban Najeriya REUTERS - Afolabi Sotunde

Sanata Lawan yace yana goyan bayan kundin tsarin mulkin Najeriya na wa’adi biyu kacal ga kowanne mai rike da kujerar shugabanci a bangaren zartarwa, kuma ba zai goyi bayan duk wani shirin sauya dokar ba.

Sanarwar tayi tsokaci kan kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da ake amfani da shi a kasar wanda ya bayyana wa’adin ofishin shugaban kasa karara, kuma ya zuwa yanzu bai ga wani dalilin yi masa gyaran fuska ba.

 

Sanarwar ta bukaci jama’a da suyi watsi da rade radin cewar shugaban Majalisar na goyan bayan sauya dokar, wanda ta bayyana shi a matsayin labarun kanzon kurege daga makiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.