Najeriya

Yanayi mai dauke da kura da iska ya hana saukar jiragen sama a Najeriya

Yanayi mara kyau da ya hana jirage sauka
Yanayi mara kyau da ya hana jirage sauka Janelle Lapointe / REUTERS

A Najeriya sabanin yadda aka saba gani, yanzu haka wani yanayi mai dauke da kura da iska mai hazo, na mamaye sassan arewacin kasar, iskan da masana ke dangantawa da canjin yanayi dake bayyana a wasu sassan duniya.  Rahotanni sun ce matsalar ta kai ga hana tashi da saukar jiragen sama a wasu yankunan kasar.Wakilin mu Shehu Saulawa ya duba wannan yanayin da aka shiga, ga kuma rahoton sa.