Najeriya

Muna murna da dawowar Super Eagles Lagos – Sanwo-Olu

Kungiyar kwallon kafar Najeriya a fadar Gwamnan Lagas
Kungiyar kwallon kafar Najeriya a fadar Gwamnan Lagas © AP - Sunday Alamba

Gwamnan Jihar Lagos dake Najeriya Babajide Sanwo-Olu ya bayyana farin cikin sa da komawar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles buga wassani a birnin bayan kwashe shekaru 20 da kauracewa jihar.

Talla

Yayin da ya karbi tawagar kungiyar da ta ziyarce shi kafin karawar da za suyi yau da kasar Lesotho a gasar neman zuwa cin kofin Afirka da za’ayi shekara mai zuwa a Kamaru, Sanwo-Olu yace mazauna Lagos na farin cikin komawar kungiyar gida, saboda muhimmancin wasannin da Jihar ke mayar da hankali a kai.

Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya
Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya © AP - Sunday Alamba

Gwamnan yace sun zuba jari sosai wajen inganta filayen wasanni domin ganin Lagos ta cigaba da jagoranci wajen harkar wasanni a Najeriya baki daya.

Sanwo-Olu ya bayyana farin cikin sa da nasarar samun tikitin da kungiyar Super Eagles ta samu kafin karawar ta yau, yayin da ya bukaci mazauna birnin da su marawa kungiyar baya domin samun nasara a fafatawar da za suyi yau da Lesotho a filin Teslim Balogun.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.