Najeriya-Tsaro

'Yan sandan Najeriya 497 sun mutu a bakin aiki cikin shekaru 6- rahoto

Wasu 'yan sandan Najeriya da ke kokarin kwantar da tarzoma a zanga-zangar adawa da muzgunawar 'yan sanda a kasar.
Wasu 'yan sandan Najeriya da ke kokarin kwantar da tarzoma a zanga-zangar adawa da muzgunawar 'yan sanda a kasar. AFP/File

Wani rahotan bincike da aka gudanar a Najeriya ya bayyana cewar jami’an 'yan Sanda 497 aka kashe lokacin da suke gudanar da ayyukan su a cikin shekaru 6 da suka gabata.

Talla

Rahotan da kungiyar SBMorgan da ke sanya ido kan harkokin tsaro ta wallafa ya ce an kuma kashe akalla fararen hula dubu 1 da 175 a hare haren da aka gani a sassan kasar daga ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2015 zuwa 22 ga watan Maris na wannan shekarar.

Kungiyar ta ce an kashe jami’an 'yan Sandan 497 sakamakon hare hare 554 da aka gani kamar yadda alkaluma daban daban suka tabbatar.

Rahotan ya ce wannan ke dada fito da matsalar tsaron da ya addabi Najeriya ganin yadda su kan su jami’an tsaron basu tsira ba.

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar ta ce an fi samun matsalar a yankin Kudu maso kudu inda aka kashe 'yan sanda 174, kuma 51 daga cikin su sun fito ne daga Jihar Delta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.