Najeriya-Amurka

Babu tabbacin Sojin Najeriya sun kashe masu zanga-zanga a Lekki -Amurka

Wani yanki na jihar Lagos a Najeriya bayan lafawar rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar ENDSARS.
Wani yanki na jihar Lagos a Najeriya bayan lafawar rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar ENDSARS. REUTERS/Afolabi Sotunde

Kasar Amurka ta sanar da cewar babu tabbaci dangane da kisan da ake zargin sojoji da aikatawa a unguwar Lekki ta jihar Lagos a Najeriya ranar 20 ga watan Oktoba da aka gudanar da zanga zangar adawa da cin zarafin 'yan Sanda.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a cikin rahotan ta na shekara shekara cewar babu tabbacin bayanai dangane da kisan da ake zargi sojojin Najeriyar sun aikata a bara.

Rahotan ya ce babu sahihanci kan mutanen da aka ce sojojin sun harbe lokacin da suka tarwatsa masu zanga zanga akan hanyar Lekkin.

Kungiyar Amnesty International ta ce mutane 10 suka mutu lokacin harbin, amma gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahotan kungiyar kuma babu wata kungiya ta daban da ta tabbatar da yawan mutanen, sai dai gwamnati ta ce mutane 2 sun mutu sakamakon lamarin.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewar sojoji sun je wurin da makamai, abinda ya sa aka kafa kwamitin bincike domin tabbatar da gaskiyar abinda ya faru.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.