Najeriya-Buhari

Dalilin da ya sa Buhari bai mikawa Osibanjo mulki ba– Garba Shehu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo. Premium Times

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai mikawa mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbaji mulki ba kafin barin kasar zuwa London inda za’a duba lafiyar sa yanzu haka.

Talla

Mai magana da yawun shugaban Garba Shehu yace dalilin rashin mikawa Osinbajo mulkin shi ne saboda lokacin da Buharin zai dauka a London bai kai kwanaki 21 da kundin tsarin mulki ya bukace shi da ya mika ragamar tafiyar da kasar ba.

Shehu ya ce a halin da ake ciki yanzu, shugaban kasar zai cigaba da gudanar da ayyukan sa na shugaban kasa a inda ya ke.

Mai magana da yawun shugaban ya ce Buhari na da cikakkiyar lafiyar da zai cigaba da jagorancin Najeriya saboda haka babu wani gaggawan mika mulki kamar yadda mutane ke magana akai.

Batun mika mulki tsakanin shugaban kasa da Gwamnonin Najeriya ga mataimakan su babban batu ne da ke haifar da cece-kuce ko da yaushe inda an samu yanayi irin wannan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.