Najeriya-Garkuwa

Garkuwa da Mutane a tsakar babban birnin Najeriya ya sake kazanta

Hanyar da tashi daga birnin Abuja zuwa Kaduna.
Hanyar da tashi daga birnin Abuja zuwa Kaduna. Daily Trust

Garkuwa da mutane na kara zama babbar matsala a kewayen garin Abuja, babban birnin tarayar Najeriya, lamarin da a yanzu ko an biya kudin fansa bashine tabbacin sakin mutanen da aka kama ba.Bayan sace daliban da akayi kwanakin baya, yanzu haka mazauna yankin na cigaba da zama cikin fargaba sakamakon karuwar satar mutanen.

Talla

Sannu a hankali matsalar garkuwa da mutane a kewayen garin Abuja musamman a yajin Abaji na kara zama babbar matsala inda ta kai jama’a sun fara kaura suna barin gidajen su don neman tsira.

Mohammed Nura ,mazaunin  unguwan hausawa a garin na Abaji, inda matsalar tafi muni, ya ce akalla zuwan karshe da sukayi sun kwashi mutum 4.

Wakilinmu ya kuma zanta da babban darakta mai kula da harkan tsaro na babban birnin tarayya malam Adamu Gwary,inda ya yi karin bayani kan matakan da ake dauka.

''Yanzu haka da nake magana dakai babban sifeton ‘yan sanda ya karawa Abuja rundunan tsaro na musamman''.

Ganin yawancin aikin kare lafiyar mutane ya rataya a wuyan jami’an ‘yan sanda ne wakilinmu ya garzaya gurin komishinan ‘yan sandan Abuja CP Bala Ciroma wanda ya ce.

''Mun duba yan kin Abaji da kyau kuma matakan da muka dauka an fara samun nasara''.

Komishinan ‘yan sandan Abujan CP Bala Ciroma ya ce idan aka yi la’akari da kokarin da su ke yi jama’a basu da dalilin kaura.

To koya kwararru a harkan tsaro ke kallon lamarin, Mohammed Sani Abubakar ya zanta da malam Salisu Dantata Mahmood, wanda ya ce abin takaici ne irin abin da ke faruwa a Abujar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.