Najeriya - Neja

'Yan bindiga 100 sun kai farmaki a sassan Shiroro dake jihar Neja

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin

Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya sun ce ‘yan bindiga afkawa wani shingen hadin gwiwar jami’an tsaron kasar na hadin gwiwa dake karamar hukumar Shiroro.

Talla

Baya ga shingen jami’an tsaron, ‘yan bindigar sun kuma afkawa kauyukan Gurmana, Bassa, Kokki da Manta da kuma Allawa da ke karamar hukumar ta Shiroro.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kone motocin soji da dama, tare da sace mutane akalla 10 da kuma babura bakwai, yayin jerin hare-haren da suke kai kan wasu kauyuka dake karamar hukumar ta Shiroro a tsakanin daren Laraba. zuwa wayewar garin yau Alhamis kamar yadda jaridar Daily Trust da ake wallafa ta a Najeriya. ta ruwaito.

Yayin tabbatar da aukuwar tashin hankalin shugaban matasan yankin Shiroro Muhammad Sani ya ce adadin ‘yan bindigar da suka kai harin ya kai kimanin 100, wadanda suka shafe sa’o’i sama da 4 suna cin karensu babu babbaka.

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumomin tsaron Najeriya ba su ce komai ba dangane da harin na baya bayan nan a jihar ta Neja, wadda ke cikin jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya da suka hada da Katsina, Zamfara, da Kaduna, da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da kuma satar jama’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.