Najeriya-Zamfara

Akwai 'yan bindiga fiye da dubu 30 a arewacin Najeriya- Gwamnan Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle.
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle. premiumtimesng

Gwamnan Jihar Zamfara da ke Najeriya Bello Mohammed Matawalle ya ce akwai akalla 'yan bindiga dubu 30 a sassan Jihar Zamfara da wasu jihohin da ke yankin arewacin kasar guda 5.

Talla

Yayin da ya ke tsokaci kan matsalolin tsaron da suka addabi jihar sa da kuma wasu jihohin arewacin kasar, Gwamnan ya ce akwai akalla sansanonin 'yan bindiga sama da 100 a jihar sa, kuma kowanne daga cikin su na dauke da 'yan bindiga sama da 300.

Gwamnan da ke magana da yawun kwamishinan yada labaran sa Ibrahim Magaji Dosara ya bayyana jihohin da wadannan 'yan bindiga su ke da suka hada da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Katsina da Kaduna da kuma Niger.

Matawalle ya ce gwamnatin Najeriya bata da sojojin da zasu iya fuskantar wadannan Yan bindiga dake yankin domin murkushe su baki daya.

Gwamnan yace yanzu haka akwai sojoji kasa da 6,000 dake yaki da 'yan bindigar a yankin arewa maso yammacin Najeriya amma duk da haka ana cigaba da samun hare hare.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.