Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta dauki alhakin kakkabo jirgin Sojin Najeriya da ya bace

Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram a Najeriya Abubakar Shekau.
Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram a Najeriya Abubakar Shekau. AP - TEL

Kungiyar Boko haram ta ce ita ce ta kakkabo jirgin yakin Najeriya wanda aka bayyana bacewar sa kwanaki biyu da suka gabata.

Talla

Mai Magana da yawun rundunar sojin saman kasar Edward Gabkwet ya gabatar da sunayen matuka jiragen guda biyu wadanda aka ce sun bata tare da jirgi, yayin da yau book haram ta fitar da sanarwar dake cewa ita ta kakkabo jirgin.

Wasu kafofin yada labaran Najeriya sun ce kungiyar ta gabatar da hotan bidiyon dake nuna jirgin na cin wuta tare da gawar wani da aka bayyana a matsayin matukin jirgin.

Bacewar jirgin sojin ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Najeriya sakamakon matsalolin tsaron da suka addabi kasar da kuma zargin rashin isassun kayan aiki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.