Gobara ta kone dukiya mai yawa a unguwar Oko Baba

Wata gobara da ta tashi
Wata gobara da ta tashi Bryn Lennon POOL/AFP

A Najeriya gobara ta kone dukiya mai yawa a kasuwar sayar da Katako dake unguwar Oko Baba, a birnin Lagos.

Talla

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun tashin gobara a kasuwar ba, wadda ke haddasa hasarar miliyoyin Nairori. A can baya dai Gwamnatin jihar Lagos tayi yunkurin sauyawa ‘yan kasuwar matsuguni amma abin ya faskara.

Tsawon shekaru ,gwamnatin jihar na kokarin ganin ta canzawa mazauna wannan wuri matsuguni ganin ta yada jama'a ke fuskantar  matsalolli a wannan unguwa da suka hada da tsaro,kiwon lafiya,wadanan wurare sun kasance maboya ga yan bata gari.

Tuni hukumomin jihar Lagas suka dau aniyar ganin sun kawo karshen zaman wadanan mazauna a unguwar Oko Baba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.