Najeriya

Hukuncin daurin ga ‘yan Najeriya da suka bijirewa yin rijistar katin dan kasa

'Yan Najeriya yayin hada hada a wani yanki na birnin Legas.
'Yan Najeriya yayin hada hada a wani yanki na birnin Legas. ASSOCIATED PRESS - Lekan Oyekanmi

Ministan sadarwar Najeriya Dakta Isa Pantami yayi gargadin cewar hukuncin daurin shekaru tasakanin 7 zuwa 14 kan iya hawa kan ‘yan Najeriya da suka bijirewa yin rijjistar katin dan kasa.

Talla

Ministan wanda ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a birnin Abuja, ya ce hukuncin daure wadanda suka yin tijistar katin na dan kasa na kunshe ne cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Shugaban hukumar fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.
Shugaban hukumar fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami. iittelecomdgest.com
A cewar Pantami, zuwa yanzu ‘yan Najeriya akalla miliyan 51 ne suka yi rijistar shaidar katin dan kasar, da ya jaddada muhimmancinsa ga gudanar lamurran yau da kullum a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.