Najeriya - Kaduna

Masu sarautun gargajiya sun tsere zuwa biranai saboda tsoro - Shehu Sani

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria

Tsohon Dan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Jihar Kaduna ta Tsakiya Sanata Shehu Sani yace tabarbarewar yanayin tsaro da jihar ke fuskanta ta tilastawa masu unguwanni da Hakimai tserewa daga yankunan su zuwa birnin Kaduna domin tsira da rayukan su daga masu garkuwa da mutane.

Talla

A sakon da ya aike ta kafar twitter, tsohon Dan Majalisar Dattawan yace yanzu haka akasarin masu unguwanni da Hakiman dake yankunan karkarar jihar sun gudu sun bar yankunan su zuwa birane domin kare kan su.

Tabarbarewar tsaro a Kaduna ta tilastawa masu unguwanni da Hakimai tserewa daga yankunan su zuwa birnin - Shehu Sani

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro musamman abinda ya shafi hare haren 'yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane suna karbar diyya.

Gwamnan jihar Malam Nasir Ahmad El Rufai ya sha alwashin murkushe yan bindigar da taimakon jami’an tsaro, yayin da yake jaddada matsayin sa na kin biyan diyya domin kubutar da wadanda akayi garkuwa da su.

Yanzu haka akwai daliban makarantar gandun dajin dake hannun 'Yan bindigar da suka kwashe su kuma suke bukatar a biya su diyya kafin a sako su, amma gwamnatin jihar tace ba zata biya ko kwabo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.