Najeriya - Nasarawa

'Yan bindiga sun kashe shugabannin kungiyar Miyatti Allah a Nasarawa

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos

‘Yan bindiga sun kashe shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah na jihar Nasarawa Alhaji Muhammad Hussaini.

Talla

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar ta Nasarawa. nasel Ramham ya ce ‘yan bindigar sun kashe shugaban Miyatti Allah na jihar ne tare da shugaban kungiyar na karamar hukumar Toto dake jihar a daren ranar Juma’ar da ta gabata.

Nasarawa na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane domin kudin fansa.

Cikin watan Janairun wannan shekara Gwamnan jihar Nasarawa Abudullahi Sule, ya koka kan cewar mayakan Boko Haram na yin tururuwa zuwa jiharsa, abinda ke taka rawa wajen karuwar barazanar rashin tsaron da suke fuskanta.

Gwamna Sule ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kaiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Abuja, inda yayi masa karin bayani kan sabuwar matsalar tsaron da ta kunno kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.