Najeriya

Najeriya ta zama dandalin kashe mutane - Bishop Kukah

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Carlo Allegri

Daya daga cikin shugabannin kiristocin Najeriya Bishop Mathew Hassan Kukah ya bayyana damuwa kan halin da kasar ta samu kan ta a yau, inda yake cewa Najeriya ta zama wani dandalin kisa daga masu aikata laifuffuka daban daban.

Talla

A sakon bikin Easter da ya gabatar, limamin Kiristan ya yi nazari kan halin da Najeriya ta samu kan ta a wannan lokaci da kuma halin da ‘yan kasar ke ciki wanda yace ya tuna masa da halin da Israila ta samu kan ta lokacin mutuwar babban limamin kasar Eli.

Najeriya na iya rasa kimarta

Bishop Kukah ya bayyana cewar yanzu haka 'Yan Najeriya na cikin tsaka mai wuya ganin yadda mayakan Boko Haram da 'Yan bindiga da masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami da wasu masu aikata laifin kisa suka sasu a gaba abinda ke haifar da fargabar cewar kasar na iya rasa kimar ta.

Limamin yace tsoffin hafsoshin soji da 'yan sanda na mamakin makomar rundunonin su ganin yadda suke fuskantar koma baya, yayin da 'Yan bindiga ke cigaba da cin zarafin 'yan kasa suna azabtar da su.

Dandalin kisa

Bishop Kukah yace ganin yadda Najeriya ta zama dandalin kisa, gwamnati da jama’ar kasar sun rasa inda zasu sa gaba, yayin da hayaki mai guba na tababa da rashin tabbas da damuwa suka addabe su.

Shugaban mabiya addinin kiristan yace yayin da jama’ar kasa ke neman kariya a daidai lokacin da bakin ciki ya dame su, an kasa samun gwamnatin da zata kare su.

Bishop Kukah yace a daidai lokacin da gwamnati ke kashe makudan kudade wajen sauya tunani da kuma mayar da tubabbun mayakan Boko Haram da 'Yan bindiga cikin jama’a, wadannan yan ta’adda da suka kaddamar da yaki a kasa na cigaba da kashe dubban mutane da lalata dukiyar su da tilastawa jama’a barin matsugunan su.

'Yan kasa basu san muhimmancin gwamnati ba

Limamin kiristan ya tambayi gwamnatin Najeriya dalilin da zai sa ‘yan kasa su cigaba da mutunta ta a daidai lokacin da take kula da lafiyar masu kashe su da kuma kassara su, yayin da su kuma aka bar su da birne ‘yan uwan su da aka kashe.

Bishop Kukah yace lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar tafiyar da Najeriya ya bayyana book haram a matsayin karamar wutar da aka bari ta girma, amma yanzu gashi a karkashin mulkin sa ana ganin wuta da dama na tashi wadanda ke neman mamaye kasar daga sassa daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.