Najeriya - Imo

'Yan bindiga sun kaiwa hukumomin tsaro farmaki a Imo

Hoton 'yan bindiga somin misali.
Hoton 'yan bindiga somin misali. © India TV News / PTI

'Yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan awaren kungiyar IPOB masu neman kafa kasar Biafra, sun kai hare-hare kan babban gidan yarin Imo inda suka saki fursunoni masu yawa.

Talla

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar adadin fursunonin da maharan suka saki ya kai kusan dubu 2. Yayin da shi kuma kakakin 'yan sandan Najeriya Frank Mba ya ce fursunoni 35 ne kawai suka rage a babban gidan Yarin na Imo, baya ga wasu 6 da suka koma da kansu.

‘Yan bindigar haye cikin akalla motoci 10 sun kuma  kone sassan Hedikawatar ‘yan sandan jihar Imo, tare da kuma kai hari kan shingen sojojin dake babbar hanyar da ta sada birnin Owerri da Onitsha, tare da kone motocinsu, bayan da jami’an tsaron suka waste.

Rahotanni sun kuma ce maharan sun kone kusan dukkanin ababen hawan dake ajiye a wuraren da suka kaiwa farmaki.

Wasu majiyoyi sun ce ‘yan bindigar da suka ci karensu babu babbaka tsawon kusan sa’o’i 2, bayan kaddamar da hare-haren da misalin karfe 1 na daren ranar Lahadi.

A baya bayan nan dai, hare-haren da ake kyautata zaton ‘yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne ke kaiwa kan jami’an tsaro a wasu sassan yankin kudu maso gabashin Najeriya sun karu.

A halin da ake ciki babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya bada umarnin farautar wadanda suka aikata ta’addancin domin fuskantar hukunci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.