Najeriya-Kaduna

Kaduna: Sojoji sun ceto dalibai 5 daga hannun 'yan bindiga

Wasu dakarun Najeriya a babban sansanin sojin kasar dake Jaji a jihar Kaduna.
Wasu dakarun Najeriya a babban sansanin sojin kasar dake Jaji a jihar Kaduna. AP - AP Photo

Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya ta sanar da cewar sojojin kasar sun yi nasarar kubutar da dalibai 5 daga cikin 39 da Yan bindiga suka sace a kwalejin koyar da aikin noma.

Talla

Kwamishinan tsaro na Jihar Samuel Aruwan ya sanar da ceto daliban yayin da yake cewa jami’an kiwon lafiya na can sun duba daliban domin tabbatar da lafiyar su.

Aruwan yace nan gaba gwamnati za tayi Karin bayani kan halin da ake ciki dangane da daliban.

A ramar 11 ga watan Maris ne Yan bindiga cikin dare suka kutsa kai makarantar koyar da aikin noman dake Afaka inda suka kwashe daliban 39.

Daga bisani Yan bindigar sun saki bidiyo dauke da daliban inda suka bukaci diyyar naira miliyan 50 kafin su sake su.

Gwamnatin Jihar Kaduna tace ba zata tattauna da Yan bindigar ba ko kuma biyan kudi domin a saki daliban.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.