Najeriya - Yan Sanda

Buhari ya nada sabon babban Sifeton 'Yan Sandan Najeriya

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Usman Alkali Baba a matsayin mukaddashin babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya, matakin da ya ce ya soma aiki nan take.

Talla

Kafin nada shi mukaddashin Sifeton na ‘yan sandan Najeriya AIG, Usman Alkali Baba na rike ne da mukamin DIG.

Ministan kula ayyukan ‘Yan Sanda a Najeriya Mohamed Maigari Dangyadi ne ya sanar da sabon nadin a yau Talata yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Ranar 4 ga watan Fabarairun da ya gabata shugaban Najeriya ya tsawaita wa’adin tsohon Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu da karin watanni 3.

Sai dai watanni biyu kawai tsohon Sifeton yayi daga cikin ukun da aka kara masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.