Najeriya - Bauchi

Sarkin Bauchi Rilwan Adamu ya nada Jonathan Jigon Bauchi

Mai Martaba Sarkin Bauchi Rilwanu Suleiman Adamu yayin bikin nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin Jigon Bauchi.
Mai Martaba Sarkin Bauchi Rilwanu Suleiman Adamu yayin bikin nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin Jigon Bauchi. © Facebook / Goodluck Jonathan

Mai Martaba Sarkin Bauchi dake Najeriya Rilwanu Suleiman Adamu ya nada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin Jigon Bauchi.

Talla

Wannan nadi na zuwa ne sakamakon ziyarar da tsohon shugaban kasar ya kai Jihar Bauchi domin kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin Bala Muhammed wadda ke karkashin Jam’iyyar PDP tayi.

Mai Martaba Sarkin Bauchi Rilwanu Suleiman Adamu yayin bikin nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin Jigon Bauchi.
Mai Martaba Sarkin Bauchi Rilwanu Suleiman Adamu yayin bikin nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin Jigon Bauchi. © Facebook / Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban ya bayyana farin cikin sa da karramawar da  gwamnatin Bauchi da Masarauta suka masa wadda ta hada da sanya sunan sa akan titin Sabon Kaura zuwa Miri.

Gwamnan Bauchi Bala Muhammed ya rike mukamin ministan Abuja a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.