Najeriya-IPOB

Sufeta Janar na Najeriya ya bada umarnin kamo mayakan IPOB

An tura jami'an tsaro zuwa Imo domin tabbatar da tsaro
An tura jami'an tsaro zuwa Imo domin tabbatar da tsaro Finbarr O'Reilly/Reuters

Babban Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya bai wa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Imo umurnin zakulo ‘Yan Awaren IPOB da suka kai hari Cibiyar ‘Yan Sandan Jihar tare da kubutar da fursunoni kusan  2000.

Talla

Kakakin ‘Yan Sandan Najeriya Frank Mba ya ce,  an kuma tura karin ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa jihar domin tabbatar da tsaro biyo bayan harin mayakan na IPOB masu dauke da muggan makamai.

Masharhanta kan lamurran tsaro irinsu Muhammad Indabawa, tsohon Kwamishina ‘Yan sanda a Najeriya ya bayyana cewa, lamurra sun dada lalacewa a kasar tun da har ana iya kaddamar da jerin hare-hare kan jami’an tsaro a yanzu.

In dai za a iya yi wa ‘yan sanda haka, to waye kuma ya rage, kuma a je a samu sojoji a yi musu abin da aka yi musu, abin sai dai a yi ta addu’a kawai, Ni ban san me ke faruwa ba .” inji Indabawa

 

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da RFI Hausa ta yi da Indabawa kan wannan batu.

Hira ta musamman kan harin da ake kai wa 'yan sanda a Najeriya

A ‘yan kwanakin nan mayakan na IPOB sun zafafa hare-harensu hatta kan ‘yan arewa da ke rayuwa a jihar ta Imo, inda suka kashe mutane 7.

Wannan matsalar tsaron na yankin kudu maso gabashin Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da yankin arewa ke fama da rikice-rikicen Boko Haram da ‘yan bindiga masu sace-sacen jama’a domin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.