Najeriya

Firsinoni 80 sun koma gidan yarin Owerri dake Najeriya

Gidan yari
Gidan yari REUTERS - EVGENIA NOVOZHENINA

Akalla firsinoni 80 daga cikin 1,844 da suka tsere daga gidan yarin Owerri dake Najeriya lokacin da Yan bindigar da ake zargin ‘yayan kungiyar Yan awaren IPOB suka kai sun koma gidan yarin da kan su.

Talla

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola da ya ziyarci gidan yarin tare da mataimakin shugaban kasa Yemo Osinbajo yace ba za’a yiwa wadanda suka kai kan su shari’a ba, amma wadanda suka gudu za’a tuhume su da laifin gudu daga inda ake tsare da su.

Mai Magana da yawun hukumar gidan yarin Joe Madugba yace firsinoni 40 suka fara komawa a ranar talata, yayin da yau laraba adadin su ya tashi zuwa 82.

Kakakin yace suna saran wasu daga cikin wadanda suka gudun su sake komawa nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.