Najeriya-Boko Haram

Haramtattun makamai sama da milyan 6 ke yawo a Najeriya - Abdulsalami Abubakar

Makamai da ake yawo da su a Najeriya
Makamai da ake yawo da su a Najeriya REUTERS - Arnd Wiegmann

Tsohon shugaban Najeriya Abdusalami Abubakar yayi shelar cewar yanzu haka akwai haramtattun makaman dake hannun jama’a wadanda bai dace ace sun mallake su ba da suka kai miliyan 6 a sassan kasar.

Talla

Yayin da yake tsokaci wajen taron masu ruwa da tsaki kan zaman lafiyar Najeriya, tsohon shugaban yace karuwar makamai sun dada zafafa matsalolin tsaron da suka addabi kasar wadanda suka yi sanadiyar hallaka rayukan mutane sama da 80,000.

Abdusalami yace matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya ayau suna da yawa sosai da suka hada da rikicin book haram da yan bindiga barayin shanu da masu garkuwa da mutane da talauci da masu bukatar raba kasa ga kuma yunwa sakamakon hana manoma zuwa gonakin su abinda ya jefa mutane cikin kakanikayi.

Tsohon shugaban mulkin sojin yace ba’a baiwa hukumomin tsaro kudaden da ya dace su gudanar da ayyukan su, kuma kowa ya san ba zasu iya aiki a wanan zamanin ba ba tare da samun makamai masu inganci ba.

Abdusalami yace fatar su itace Najeriya ta samo hanyar shawo kan wadannan matsaloli ta hanyar tintiba da kuma sauraron shawarwari wadanda zasu taimaka wajen karfafawa jama’a gwuiwa.

Tsohon shugaban yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na da labarin taron da suke yi kuma ya bayyana goyan bayan sa akai.

A nashi jawabi tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya bukaci al’ummar kasar da su kauda banbancin addini da kabila da kuma siyasa domin taimakawa wajen shawo kan wadannan matsalolin da suka sha kan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.