Najeriya-'Yan sanda

Yemi Osinbajo ya makalawa Usman Baba sabon mukamin sa na Sufeto Janar

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yayin makalawa sabon babban sufeton 'yansanda na kasar Usman Alkali Baba sabon mukaminsa.
Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yayin makalawa sabon babban sufeton 'yansanda na kasar Usman Alkali Baba sabon mukaminsa. © Presidency / Femi Adesina

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya makalawa sabon Sufeto Janar na Yan Sandan Usman Alkali Baba sabon mukamin sa kasa da sa’oi 24 bayan nadin da aka masa.

Talla

Yayin wani biki da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja, Farfesa Osinbajo tare da Babban Hafsa a Fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari sun likawa Baba sabon mukamin sa wanda zai cigaba da rikewa har zuwa lokacin da Majalisa koli ta kasa zata tabbatar masa da mukamin.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo bayan kammala makalawa sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba mukaminsa.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo bayan kammala makalawa sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba mukaminsa. © Presidency / Femi Adesina

Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin harda Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da tsohon Sufeto Janar mai barin gado Adamu Muhammad da ministan Yan Sanda Maigari Dingyadi da Babban Sakatare a ma’aikatar Temitope Fashedemi.

Kafin nadin na sa sabon Sufeto Janar din na jagorancin sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar Yan Sanda ta kasa dake Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.