Najeriya-Imo

'Yan bindiga sun sake far wa shalkwatan 'yan sanda a Imo

Hare-haren da ake kai wa gine-ginen 'yan sanda a Imo sun tsananta
Hare-haren da ake kai wa gine-ginen 'yan sanda a Imo sun tsananta AFP

‘Yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan IPOB ne, sun sake kaddamar da farmaki kan shalkawatan ‘yan sanda da ke Karamar Hukumar Mbaitoli ta jihar Imo a Najeriya a safiyar Alhamis din nan tare da sace wani jami’in tsaro.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan  kwanaki uku da ‘yan bindigar suka kai makamancin wannan farmakin kan shalkwatan ‘yan sandan da kuma Gidan Yarin Gyara Halinka na garin Owerri tare da kubutar da fursunoni  dubu 1 da 884.

Kazalika tsagerun sun sake kubutar da fursunoni a harin na yau kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito daga shaidun gani da ido.

Rahotanni na cewa, jami’an ‘yan sanda sun yi dauki-ba-dadi da  ‘yan bindigar masu rike da muggan makamai, abin da ya sa suka fi karfi jamian tsaron.

Gwamnatin Najeriya ta lashi takobin hukunta tsagerun da ke kai wa 'yan sanda hari

Jami’in Yada Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Imo, Orlando Ikeokwu ya tabbatar da farmakin na baya-bayan nan duk da cewa bai yi cikakken bayani ba kawo yanzu.

‘Yan sanda na zargin haramtacciyar Kungiyar IPOB mai fafutukar neman kafa kasar Biafra da kaddamar da hare-haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.