An kashe sojojin Najeriya a Benue
Wallafawa ranar:
Rundunar sojin Najeriya ta ce an kashe dakarunta 11 a wani harin da aka kai masu a yankin Konshisha cikin jihar Benue da ke tsakiyar kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters da ya ruwaito wannan labari, da farko ya jiyo kakakin rundunar tsaron Mohammed Yarima na cewa sojojin sun bata a daidai lokacin da suke gudanar da sintiri, to amma daga bisani an tsinci gawarwakinsu.
Rundunar ta ce, za ta zakulo mutanen da suka aikata wannan danyan aikin domin yi musu hukuncin da ya dace da su.
Rahotanni na cewa, tuni wasu daga cikin fararen hula suka fara tserewa daga Karamar Hukumar ta Konshisha saboda fargabar abin da ka iya biyo baya.
Hare-hare kan jami’an tsaro a Najeriya sun tsananta a baya-bayan nan, domin kuwa ko a cikin wannan makon sai da aka far wa sojoji a shingayen binciken ababawan hawa a jihar Imo da ke kudo maso gabashin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu