Najeriya - Boko Haram

ISWAP ta kai hari cibibiyoyin bada agaji a Damasak dake Barno

Wata motar yaki na mayakan Boko Haram da sojojin Najeriya suka kwace a jihar Barno
Wata motar yaki na mayakan Boko Haram da sojojin Najeriya suka kwace a jihar Barno AFP Photo/AUDU MARTE

Bangaren Boko Haram dake da alaka da kungiyar IS a Najeriya wato ISWAP ta kai hari cibiyoyin ba da agaji a garin Damasak da ke jihar Barno a arewa maso gabashin kasar.

Talla

Majiyar ma’aikatan agajin ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar, Mayakan  (ISWAP) da suka mamaye Damasak dake jihar Borno, sun cinna wuta a cibiyoyin kungiyoyin agaji na kasa-da-kasa.

"Mayakan ISWAP har yanzu suna cikin garin Damasak, suna ta zirga-zirga a kan tituna, suna ta harbe-harbe da kuma cinnawa wuraren jin kai wuta," in ji wani ma'aikacin agajin da ya nemi a sakaya sunansa.

Wata majiya kuma tace, Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ta kone ne, bayan da aka cinna wuta a ofishin wata kungiyar agaji ta kasa da kasa dake kusa da ita.

Haka kuma maharan da suka mamaye garin sun kona ofisoshin wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda uku na kasa da kasa.

Wata majiyar soji ta tabbatar da harin na ranar Asabar a Damasak amma ta ce mayakan sun kasa mamaye garin.

Harin, wanda aka kai da yammacin ranar Asabar, shi ne na biyu cikin watanni biyu da ke shafar daya daga cikin cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya guda tara  dake kasar.

Harin Boko Haram ta saba kai hari kan kaya da ma'aiktan agaji

A ranar 1 ga watan Maris, mayakan ISWAP sun mamaye wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Dikwa, inda suka kashe fararen hula shida tare da tilasta wa ma’aikatan agaji ficewa na wani lokaci duk da bukatun agajin gaggawa da ake fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.